Jihar Zamfara jiha ce da ke arewa maso yammacin ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita 39,762 da yawan jama’a kimanin mutane 3,838,160 (miliyan uku da dubu ,ɗari takwas da talatin da takwas da ɗari ɗaya da sittin) (jimillar ƙidayar shekara ta 2011)[1]. Babban birnin tarayyar jahar shi ne Gusau[2]. Bello Matawalle[3] shi ne gwamnan jihar tun hukuncin da kotu ta yanke a matsayin gwamnan jihar ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC, shi ne ya bashi damar zama gwamnan ta a shekara ta 2019, har zuwa shekara ta 2023, Inda aka yi sabon zaɓe Kuma Dauda Lawal [4]ya karɓi Mulki a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023.

Zamfara
Zamfara State (en)


Wuri
Map
 12°10′N 6°15′E / 12.17°N 6.25°E / 12.17; 6.25
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birniGusau
Yawan mutane
Faɗi4,515,427 (2016)
• Yawan mutane113.56 mazaunan/km²
Harshen gwamnatiTuranci
Labarin ƙasa
Yawan fili39,762 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyijihar Sokoto
Ƙirƙira1 Oktoba 1996
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwaexecutive council of Zamfara State (en) Fassara
Gangar majalisaZamfara State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2NG-ZA
Wasu abun

Yanar gizozamfara.gov.ng
Tambarin Gwamnan jihar Zamfara
tambarin jihar zamfara
Talata mafara post ofis
Zamfara state gallery at arewa house museum Seal of zamfara state government
Kyau yan zamfara
wuri a zamfara
zamfara gusau
Gusau

Tarihi.

gyara sashe

Asalin Zamfarawa

mutanen zamfara sun kasance maharba ne su a lokacin baya

Zamfara ta kasance ɗaya daga cikin masarautun asali na Hausawa. zamfarawa asalin Hausawa[5]a. Sarkin musulmi [6]Muhammadu yana ganin Zamfarawa sun samu asali ne daga uba Bakatsine da uwa Bagobira. To su Zamfarawa sun kafa asalinsu ne daga Maguzawa maharba waɗanda sun zauna a yankin ƙasar Kano kafin zuwan Bagauda tun kafin zuwan Barbushe a Dutsen Dala. A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa Hausawa ne na asali tun can fil azal. Zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa dai asalinsu maharba ne daga Maguzawa. Watakila sun samu tasirin Bare-Bari a farkon tarihinsu ko kuma a ce Bare-bari ne na asalin sarautar Zamfara. Tarihin ƙauyen Zamfara ya samo asali ne daga mutum Na farko da ya fara zama a cikin garin, daga garin ZAMFARA wanda ake kira da BAWA. Shi ya sa ake kiran garin da suna Zamfara. Farkon fadar masarautan an rusa ta. Garin ya haɗa iyakoki kamar haka; Rogo sabon gari da,Tsohuwar Rogo ta gabas, Bari da Kaduna daga gefen yamma, Kaduna daga Kudu da Gari da Tsohuwar Rogo ta arewa.[7]

Ana ganin Zamfarawan asali wasu irin manya-manyan mutane ne, a taƙaice dai Samudawa ne. Dakka, sarkin Zamfara na farko kamar dai Barbushe yake, mutum ne mai tsananin girma da ƙarfi da jarumta. Akwai wasu manya-manyan kaburbura guda shida a Dutsi waɗanda aka ce kaburburan sarakunan Zamfara ne na asali. Sabo da girman kaburburan su ana kiransu da kaburburan Samudawa. Ga alamu Zamfarawa asali na da girman jiki sosai.

Birnin Zamfara

Fayil:Mtkwatarkwashi 4.jpg
dotsen kwatarkwashi

Zamfarawa sun fara kafa garinsu na farko ne mai suna Dutsi a ƙasar Zurmi ta yanzu. Don haka har yau Sarkin Zurmi na amsa sunan Sarkin Zamfara. An ce Zamfarawa sai da suka kwashe shekaru bakwai ba su naɗa sarki ba a Dutsi,daga nan sai suka naɗa sarkinsu na farko mai suna Dakka. Domin haka Sarkin Zamfara ana masa take da gimshikin gidan Dakka. Sarakuna huɗu ne suka gaji Dakka a Dutsi. Daga nan sai sarauniyar 'ƴar Goje.

Zamfara
Zamfara road

Daga Dutsi sai Zamfarawa suka yi tafiyar kamar mil talatin a kan gulbin Gagare kusa da garin Isa na yanzu suka kafa wani sabon gari mai suna Birnin Zamfara. An ce Sarkin Zamfara na bakwai mai suna Bakurukuru ya kafa birnin. Amma wasu masana tarihi sun hakikance cewa sarakuna ashirin da uku 23 ne aka binne a garin Dutsi don haka ba dai sarki na bakwai ba wanda ya kafa Birnin Zamfara. Zamfarawa sun gina garinsu wanda ya habaka sosai. Sun katange shi da ganuwa. Har yanzu akwai kufan tsohon garin akwai rusasshiyar ganuwa mai tsawon milyan goma-sha-uku da kofofin gari hamsin. A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa sun kafa garinsu na biyu wanda ya kasance babbar cibiyar mulkin Zamfara. Sannan garin ya samu arziƙin masarrafofin zamani irin su Makarantun Boko, islamiyya, rijiyoyi, Burtsatse da dai sauransu.[7]Ofishin siyasa ta mata an buɗeta ne a garin zamfara a shekarar 2007. [8]

Kananan hukumomi

gyara sashe
  1. Anka
  2. Bakura
  3. Birnin-Magaji/Kiyaw
  4. Bukkuyum
  5. Bungudu
  6. Gummi
  7. Gusau
  8. Kaura-Namoda
  9. Maradun
  10. Maru
  11. Shinkafi
  12. Talata-Mafara
  13. Tsafe
  14. Zurmi

Rufe Netwok A Jihar Zamfara

gyara sashe
Zamfara coat of arm

A ranar 3 ga watan satumba na shekarar 2021, gwamnatin Jihar zamfara ta bada umarnin kulle dukkan layukan wayar hannu (sim card) da sabis na ɗaukacin Jihar zamfara gaba ɗaya don a samu a magance matsalar tsaro. Anyi hakan ne domin yaƙi da 'ƴan Bindiga Daɗi da kuma 'Yan ta'adda. An bada umarnin rufe sabis ɗin ne na tsawon sati Biyu domin dawo da zaman lafiya da tsaro me ɗorewa a jihar ta Zamfara.[9]

Arziki

gyara sashe

tattalin arzikin Zamfarawa ya ta, allaƙane da harkar noma da kuma kiwo, sannan kuma da kasuwanci.

Tsaro

gyara sashe

Wasanni

gyara sashe

Mutane

gyara sashe

Mataimakin gwamnan shi ne Mahadi Ali Gusau. Dattijan jihar su ne: Janar Aliyu Muhammad Gusau me Ritaya,Ahmad Rufai Sani, Mamuda Aliyu Shinkafi, Abdul'aziz Abubakar Yari,Hassan Nasiha,Sahabi Liman Kaura, Mansur Dan'Ali,Kabir Garba Marafa, Dauda Lawal Dare, Sadiya Umar Farouq da Tijjani Kaura.

Taswira Najeriya, inda jan yake nanne jihar Zamfara (Gusau)

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bing.com/ck/a?!&&p=a556518742b7c156JmltdHM9MTcxOTQ0NjQwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTQzOA&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=population+of+zamfara+state+2011&u=a1aHR0cHM6Ly93d3cuZmFjdHMubmcvbmlnZXJpYW4tc3RhdGVzL3phbWZhcmEvIzp-OnRleHQ9WmFtZmFyYSUyMGhhcyUyMHR3byUyMG1ham9yJTIwZXRobmljJTIwZ3JvdXBzJTJDJTIwSGF1c2ElMjBhbmQsYW4lMjBlc3RpbWF0ZWQlMjBwb3B1bGF0aW9uJTIwb2YlMjAzJTJDODM4JTJDMTYwJTIwYXMlMjBhdCUyMDIwMTEu&ntb=1
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailypost.ng/2024/06/23/gusau-cargo-airport-absurd-inconceivable-shinkafi-to-gov-lawal/&ved=2ahUKEwjGwJvM5vGGAxV5XEEAHcOPBT8QxfQBKAB6BAgGEAE&usg=AOvVaw2BUsg3-pX1t7Al-lIbd68v
  3. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://defence.gov.ng/2023/12/31/the-honourable-minister-of-state-for-defence-dr-muhammed-bello-matawalle-mon-in-company-of-the-minister-of-humanitarian-affairs-and-poverty-alleviation-dr-betta-edu-and-the-service-chiefs-in-plateau/&ved=2ahUKEwjB8_-cvvCGAxUwV0EAHexvAM4QxfQBKAB6BAgLEAI&usg=AOvVaw2zh8vDmF1gUY_sE6-eiPVy
  4. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailynigerian.com/gov-lawal-upgrade-zamfara/&ved=2ahUKEwjZquzSvvCGAxWlXUEAHTSyB-kQxfQBKAB6BAgGEAE&usg=AOvVaw0Bcwg4oPpF1MxR-kPc42ca
  5. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://trtafrika.com/ha/africa/tashe-aladar-hausawa-lokacin-ramadan-17603105&ved=2ahUKEwj97MeRv_CGAxVVUUEAHYrSBCYQxfQBKAB6BAgMEAI&usg=AOvVaw2tqxPhOk-rB6iUbdwJ_ebE
  6. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://amp.dw.com/ha/musulmi-na-gudanar-da-babbar-sallah-ta-2024/a-69376621&ved=2ahUKEwj0hKHx5vGGAxUZXUEAHd_xAfoQyM8BKAB6BAgJEAI&usg=AOvVaw1anRUPTy7Py8jCPqpn1W_s
  7. 7.0 7.1 G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History of karaye. p.71 ISBN 978125341
  8. Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. p.164ISBN 978-978-906-469-4
  9. https://punchng.com/banditry-months-after-no-fly-order-fg-shuts-down-telecom-sites-in-zamfara/
  • Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.
  • Bello, Ahmadu, Sir, 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu, Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman. Ismaila., Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
  • G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History.of karaye. ISBN 978125341


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara