Maryam Hiyana
Maryam Hiyana tsohuwar jaruma a masana'antar Kannywood ,Maryam Hiyana jaruma ce da ta yi tashe a shekarun baya , ta Dade tana fim daga baya tai aure, tayi tashe a lokacin ta , kyakkyawar doguwar mace ,a zamanin ta tana daya daga cikin kyawawan mata a masana antar,tayi zamani dasu Fati Muhammad, Kubra Dako, Jamila Nagudu.[1].
Maryam Hiyana ta fito a Fina-finai da dama irin su Hiyana,Tutar So,Na Goma da sauran su.
Takaitaccen Tarihin Tagyara sashe
Maryam usman hiyana (maryam olomi ko Kuma maryam hiyana) ta samo sunan hiyana ne a sanadiyyar fim din datayi Mai suna hiyana shine fim dinta na farko a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud ,tayi fim din tare da manyan jarumai Sarki Ali Nuhu da Kuma Adam A Zango, Ahmad S Nuhu, Jamila Umar Nagudu , Ahmad Sadiq, Wanda babban Mai Bada umarni a masana'antar fitaccen a fannin Ashiru Nagoma.daga wannan fim din ake Kiran ta da Maryam hiyana.[2].jarumar tayi aure bayan Wani ibtila,I ya fada mata a harkan fim inda tai aure Kuma tana zaune lafiya a gidan mijin ta inda ta haifi Yara biyar dashi. Tayi aure bayan Wani iftila'i ya fada mata na Kaddarar rayuwa. Tayi aure inda ta auri Ado Ahmad dangulla. Shine masoyi daya aure ta bayan wnnn iftila'i daya sameta a rayuwar ta. Ya aure ta ya riketa da Amana . A yanzun haka jarumar tana da Yara guda biyar tare da maigidanta Ado Ahmad dangulla cikin inuwar aure.
Fina finan tagyara sashe
- Hiyana
- Tutar so
- Babban gari
- Ahali
- Da sauran su