Dauda Kahutu Rarara
Mawakin siyasa
Dauda Adamu Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara, an haife shine a ( jihar Katsina ) shahararren mawaƙin ƴan siyasa ne a Nijeriya, mawaƙi a fannin rera waƙoƙin yan siyasa kuma marubucin wakoki, Ni Abdussamad nace Dauda Kahutu Rarara yafi kowa kudi a masana'antar Kannywood.[1] wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen rera waƙoƙin ƴan jam'iyar(APC) All Progressive Congress a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2015, musamman ma ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari[2] da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari.[3].
![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Katsina, 13 Satumba 1986 (37 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƙabila | Musulunci |
Karatu | |
Harsuna | Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Kyaututtuka | gani
|
Rayuwar farko da ilimigyara sashe
An haifeshi ne a jihar Katsina a wani kauye da ake kira Kahutu, Yayi karatun Alqur'ani a makarantar Almajiranci, wata hanyar gargajiya ce ta Hausawa ta koyon addinin Musulunci.wato (kolanta).
Siyasagyara sashe
Rarara ya kasance sananne ne yayin babban zaben Najeriya na 2015, lokacin da yake rera wakoki da dama ga Muhammadu Buhari da kuma adawa da shugabancin Goodluck Jonathan a galibin wakokin nasa. A watan satumba na 2020, Rarara ya nemi gudummuwa daga masoyan Muhammadu Buhari, don tura masa Naira dubu daya domin sakin bidiyon minti biyu na yabon Muhammadu Buhari, cikin kasa da awanni 48 Ya karbi Naira miliyan 57 don sakin wakar wacce Ya yaba Muhammadu Buhari.
Wakokinsagyara sashe
Dauda kahutu rarara yayi wakoki da dama, ga kaɗan daga cikin fitattun wakokinsa;
- Masu Gudu-su-Gudu
- Buhari ya Dawo
- Baba Buhari dodar
- Jahata ce
- Kwana ɗarin Dallatu
- Kano ta Gandujace
- Ubban Abba zama daram
Shugaban 13x13gyara sashe
Shine shugaban kungiyar matasan kannywood ta 13x13, wata kungiya ce ta adadin mutum sha ukku (13), kuma ko wanne mutum daya daga cikin su sha ukkun yana da mutum 13 dake ƙarkashinsa.[4]
Sukargyara sashe
Wasu futattun matasa sun afkawa Rarara yayin da yake daukar bidiyo a jihar Katsina. Ana zargin sa da wawure Naira Miliyan 100 da jam'iyyar siyasa ta All Progressive Congress ta ba wa duk wadanda ke rera wakoki ga ƙungiyar siyasa.[ana buƙatar hujja]
.
Manazartagyara sashe
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/media-54174138
- ↑ https://www.duhocchina.com/baike/en/Dauda_Kahutu_Rarara#cite_note-2
- ↑ https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/dauda-kahutu-rarara-songs-sabuwar-wakar-rarara-a-kotun-ma-ganduje-ne-a-inec-ma-ganduje-ne-wakokin-rarara-rarara-abba-zaman-gida-dole-rarara-ganduje-rarara-masari-rarara-buhari-download-wakokin-rarara-mp3-songs.html
- ↑ https://fimmagazine.com/cewar-rarara-a-taron-13x13-za-mu-iya-ciyar-da-mutum-miliyan-gomaidan-[permanent dead link]mun-ha%C9%97a-kai/