Annabi Musa (a.s) yana daya daga cikin manyan annabawa masu daraja ta daya, da Allah (S.W.A) ya ba mu labarinsu a cikin Alƙur'ani mai tsarki. Yana daga cikin mu'ujizoji babba, ya rayu a lokacin da ake kashe duk wani yaro da aka haifa daga Banu Isra'il lokacin Firauna ibn Musab a ƙasar Misra.

Annabi Musa
Annabawa a Musulunci
Bayanai
Jinsinamiji
SunaMoses
Suna a harshen gidaمُوسَى‎
Shekarun haihuwa1392 "BCE"
Wurin haihuwaMisra
Lokacin mutuwa1272 "BCE"
Wurin mutuwaMoab (en) Fassara
UbaAmram (en) Fassara
UwaJochebed (en) Fassara
DangiHarun (en) Fassara
Muƙamin da ya riƙeAnnabawa a Musulunci
Wanda ya biyo bayanshiHarun (en) Fassara

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

Annabi musa, amincin Allah ya tabbata a gare shi, yana cikin qabilar banu isra'ila ne. A masar aka haife shi, a zamanin wani fir'auna da ake kira Alwalidu ibn musab-ibnal-rayyar. haka aka ruwaito shi cikin littafin da ake kira Hazinu, sunan mahaifin Annabi musa imrana. A lokacin su bani isra'ila suna ƙarƙashin daular wannan fir'aunu ne, sarkin masar. shi kuwa wannan fir'auna, ba abin da ya qi, kamar wannan qabila ta yahudawa, bani isra'ila. ga su a ƙarƙashinsa, amma kamar suna qarqashin wuta. azaba kusan ba irin wadda ba shi gwada musu. hasali ma abin har ya kai ya da oda, in yahudawa sun haifi namiji, to sai yace a yanka shi, Wai don wani boka ya gaya masa cewa za a haifi wani jinjiri a cikinsu wanda zai ɓata masa mulkinsa. amma idan sun haifi mace wannan ita ba ya yanka ta. Ana nan haka, sai wata mace, a cikin yahudawa watau matar imrana ta haifi d'a, aka sa masa suna Musa. Shine kuma annabi musa da zamu baku labarinsa a yanzu. Da uwarsa ta haife shi, sai tsoro ya cika ta, ga shi ya fito namiji. ba mace ba, watau fir'una zai sa ke nan a zo a kama shi a yanka, kamar yadda ake yanka sauran "ya "yansu maza. tana cikin wannan zulumi, mai baqanta rai sai madaukakin sarki Allah ya aiko mata da ilhami aka ce mata ta sami akwati, ta saka jinjirin a ciki ta rufe, ta dauka ta je ta jefa shi cikin kogin nilu.shi ke nan sai ta zabura ta bi umarnin mahaliccinta da ta jefa shi a kogi ta dawo gida sai ruwa ya yi ta tafiya da shi, Ubangiji ya yi mata alqawarin zai mayar mata da shi, ya kuma sanya shi cikin Manzanni, bisa ga nufin Madaukakin Sarki Allah.ya kuma sanya shi cikin manzanni, bisa ga nufin Madaukaki sarki Allah, har ruwan ya kai akwatin kusa da birnin Fir'auna, sai akwati ya sarqafe a gefen kogi. shi ke nan, wadansu jama'ar fir'auna sun zo diban ruwa sai ga akwati, suka dauka suka kai wa matar fir'auna. Daga aka fasa akwati sai ga jariri ciki, da ransa kuwa, ba matacce ba. Daga nan sai matar fir'auna ta dube shi tayi mamaki, ta ce kada a kashe shi, qila in ya girma ya zama mai amfani a gare mu, ko kuwa ma mu riqe shi kamar mu muka haife shi: Shi ke nan, Annabi Musa yayi ta girma a cikin birnin fir'auna. Mun gaya muku kuwa tun baya, irin zaman da jama'ar su Annabi Musa, wato bani isra'ila suke yi a qarqashin daular fir'auna. Hasali ma dai yahudawa alokacin sune kamar bayi na mutanen masar. Ana nan a haka, da Annabi Musa fa ya kawo qarfi, sai ya fara tunanin yadda zai taimaki yahudawa, har ya cire musu wannan qangi na bauta, da qasqanci da azaba, wadanda suke samu daga fir'aunya kuma sanya shi cikin manzanni, bisa ga nufin Madaukaki sarki Allah, har ruwan ya kai akwatin kusa da birnin Fir'auna, sai akwati ya sarqafe a gefen kogi. shi ke nan, wadansu jama'ar fir'auna sun zo diban ruwa sai ga akwati, suka dauka suka kai wa matar fir'auna. Daga aka fasa akwati sai ga jariri ciki, da ransa kuwa, ba matacce ba. Daga nan sai matar fir'auna ta dube shi tayi mamaki, ta ce kada a kashe shi, qila in ya girma ya zama mai amfani a gare mu, ko kuwa ma mu riqe shi kamar mu muka haife shi: Shi ke nan, Annabi Musa yayi ta girma a cikin birnin fir'auna. Mun gaya muku kuwa tun baya, irin zaman da jama'ar su Annabi Musa, wato bani isra'ila suke yi a qarqashin daular fir'auna. Hasali ma dai yahudawa alokacin sune kamar bayi na mutanen masar. Ana nan a haka, da Annabi Musa fa ya kawo qarfi, sai ya fara tunanin yadda zai taimaki yahudawa, har ya cire musu wannan qangi na bauta, da qasqanci da azaba, wadanda suke samu daga fir'auna.wannan tausayi na Annabi Musa zuwa ga jama'arsu ta bani Israil.

Dalilin Aikoshi

gyara sashe

Haƙika Allah (S W A) ya aiko Annabi Musa kamar yadda yake aiko sauran annabawa, tundaga kan Annabi Nuhu zuwa kan Annabi Muhammad (s.a.w).Allah ya aikoshi da Tauhidi kamar yadda sunan annabawa ta gabata, zuwa ga Banu Isra'il sukaɗai kamar yadda Alƙur'ani mai girma yabamu labari, saɓanin annabi Muhammad wanda Allah ya Aikashi zuwa ga kowa da kowa.

Mu'ujizozinsa

gyara sashe

cikin ayoyin Alkur’ani mai girma, an bayyana mu’ujizozi guda 9 ga Annabi Musa, wadanda suka hada da: sandar da ta koma wani katon maciji, da hasken hannun Musa, da guguwar tsawa, da fari da suka mamaye filayen noma, aphids (a. nau'in kwarin tsire-tsire), kwadi (kwaɗin da Kogin Nilu ya tashi), jinin Nilu, fari da rashin 'ya'yan itace iri-iri, da Fir'auna da sojojinsa suna nutsewa cikin kogin Nilu.[1][2]

Manazarta

gyara sashe