Hadiza Aliyu

'Yar fim

Mukala mai kyau

Hadiza Aliyu wacce akafi sani da Hadiza Gabon (An haife ta ranar ɗaya 1 ga watan Yuni, 1989) a ƙasar Gabon,[1] Hadiza Aliyu ta Kasance Shahararriyar 'yar wasan kwaikwayo ce a Hausa film a Najeriya, a ƙarƙashin masana'antar film ta Hausa kannydwood.

Hadiza Aliyu
Rayuwa
Cikakken sunaHadiza Aliyu
HaihuwaLibreville, 1 ga Yuni, 1989 (34 shekaru)
ƙasaNajeriya
MazauniKaduna
Harshen uwaHausa
Fillanci
Karatu
HarsunaTuranci
Hausa
Larabci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'aJarumi
Imani
AddiniMusulunci
IMDbnm8040689
hadizaaliyu.com

Farkon Rayuwagyara sashe

An haifi Hadiza Aliyu Gabon ne a ƙasar Libreville da ke ƙasar Gabon, ta dawo kasar mahaifiyar ta Najeriya daga bisani domin wasu dalilai, inda tayo karatu, sannan ta fara harkan fim, Haifaffiyar garin Libreville, Jamhuriyar Gabon,[2] Hadiza Aliyu ‘yar gidan Malam Aliyu ne wanda dattijo ne. A ɓangaren mahaifinta, Hadiza 'yar asalin ƙasar Gabon ce, kuma a bangaren mahaifiyarta, asalin ta Fulani ce daga jihar Adamawa, Najeriya.[3]

Ilimigyara sashe

Hadiza Aliyu ta halarci makarantun firamare da sakandiri a ƙasar haihuwarta inda ta rubuta jarabawarta ta A-Level tare da burin zama lauya sannan daga baya ta zabi Lauya a matsayin kwas din da ta fi so. Ta fara karatun jami'a a matsayinta na daliba, amma dole ta daina zuwa makaranta saboda wasu matsaloli da suka dabaibaye karatun nata . Karatun nata ya tsaya a lokacin kuma hakan ya ba ta damar halartar shirin difloma a cikin Harshen Faransanci kuma daga baya ta zama malama mai koyar da Faransanci a wata makarantar sirri.[4]

Shaharagyara sashe

Tana daya daga cikin manyan jarumai mata a masana'antar fim ta kannywood, dake arewacin nigeria. Tana da masoya da dama , tayi fina finai shaharrru a masana'antar. Ta fito a fim mai dogon zango na tashar Arewa 24 mai suna GIDAN BADAMASI, ta kuma fito a shahararren fim mai dogon zango MANYAN MATA. A halin yanzu ta bude wani filin tattaunawa da manyan mutane Sannan nu mai suna GABONS ROOM TALK.

Fimgyara sashe

Hadiza Aliyu ta shiga Kannywood ba da dadewa ba bayan ta shigo daga Gabon zuwa jihar Adamawa, Najeriya . Ta tashi daga Adamawa zuwa Kaduna yayin da take sha'awar shiga masana'antar fim ta kannywood tare da dan uwan ta. Ta samu damar ganawa da Ali Nuhu kuma ta nemi taimakonsa don kaddamar da ita a matsayin 'yar fim. Hadiza ta fara fitowa ne a shekara ta 2009, inda aka sanya ta a Artabu, ta samu shiga masana'antar fim ta kannywood a matsayin daya daga cikin manyan jarumai mata tare da taimakon Ali Nuhu da kuma jagorancin Aminu Shariff . Ta kasance shahararriyar 'yar wasan Hausa ce. Mutane da dama na gani da daukan ta a matsayin jarumar 'yar wasan Kannywood kuma abar koyi musamman yadda take fitowa cikin sutura na al'ada da kyau, tana fitowa a wasannin barkwanci na ban dariya.[5] Hadiza ta kasance ita ce jakadiyar da ta daga cikin kamfanin sadarwa na Najeriya MTN Nigeria da kuma kamfanin abincin Indomie, ta karbi kyautar Best Actress Jury Award a 2nd Kannywood Award wanda kamfanin MTN Najeriya suka dauki nauyin bayarwa. Ita ce wacce ta kafa gidauniyar HAG Foundation.[6][7][8][9][10][11]

Hadiza ta yanke shawarar shiga Nollywood a shekara ta 2017, biyo bayan Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Yakubu Muhammed, Maryam Booth da Rahama Sadau . An saka ta a fim dinta na farko na Nollywood kusa da Mike Ezuruonye, Mike Angel da Emmanuella a fim mai taken Lagos Real Fake Life .

Jakadancigyara sashe

A watan Disambar shekara ta 2018 ne, kamfanin NASCON Allied Plc,[12] wanda ke reshen rukunin kamfanonin Dangote , ya bayyana Hadiza Aliyu a matsayin jakadiyar jakadancin Dangote Classic Seasoning a yayin kaddamar da kayan hada kayan a Kano.[13][14][15]

Taimakogyara sashe

A shekara ta 2016, Hadiza ta kafa ƙungiyar agaji mai suna HAG Foundation Da nufin inganta rayuwar talakawa ta hanyar samar da taimako a bangarorin ilimi da kiwon lafiya gami da wadatar abinci, Ta zama daya daga cikin ‘yan wasa mata na farko a tarihin Kannywood da ta gabatar da irin wannan taimakon jin kai.

A watan Maris na shekara ta 2016, ta ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijirar da ke cikin jihar Kano inda ta ba da gudummawar kayayyakin abinci, kayan masaka da sauran kayan masarufi da mazauna sansanin suke bukata saboda rikicin arewacin Najeriya.[16]

Lamban girmagyara sashe

Hadiza Aliyu ta samu kyaututtuka da girmamawa da dama wadanda suka hada da shekara ta 2013 Best of Nollywood Awards da 2nd Kannywood / MTN Awards a 2014. Saboda karramawar da ta yi a matsayin 'yar fim, Hadiza ta karrama a shekarar 2013 daga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso . An kuma ba ta lambar yabo ta Hollywood ta Afirka a matsayin Jarumar Jarumai mata .

Awadgyara sashe

Lamban girman da Hadiza Aliyu Gabon ta samu[17]

YearLamban girmaRukuniFimSakamako
2013Kwankwasiyya AwardRecognition AwardKwankwasiyya AwardLashewa
20132013 Best of Nollywood AwardsBest Actress (Hausa)Babban ZaureLashewa
2014City People Entertainment AwardsBest Actress (Hausa)[18]Babban ZaureAyyanawa
20142nd Kannywood/MTN Awards[19]Best Actress of the Year(Jury Choice)[20]Daga Ni Sai KeLashewa
2015Kannywood AWA 24 Film & Merit AwardBest Supporting ActressAli Yaga AliLashewa
2016African Hollywood AwardsBest Actress[21]African Films in Hausa LanguageLashewa
2017Arewa Night AwardRecognition AwardLashewa
20172017 Best of Kannywood AwardBest Actress (Hausa)[22]Ayyanawa

Kyaututukagyara sashe

Jadawalin kyaututtukan martabawa da Hadiza Aliyu Gabon ta samu

YearGirmamawaRukuniBangare
2016Kano State Senior Secondary Schools Management BoardCertificate of Appreciation[23]Educational Support
2016Statup KanoCertificate of Appreciation[24]Empowerment Support
2016Billycares Charity FoundationRecognition AwardPhilanthropy
2019Hausa Students Association of Nigeria (BUK)Recognition AwardEducational Support

Fina finaigyara sashe

Fina finan ta
ShekaraSunan FimMatsayinNau'i
Daina KukaJarumaFim
Farar SakaJarumaFim
Fataken DareJarumaFim
KoloJarumaFim
MukaddariJarumaFim
SakayyaJarumaFim
Umarnin UwaJarumaFim
ZiyadatJarumaFim
2009ArtabuJarumaFim
2010WasilaJarumaFim
2010Umarnin UwaJarumaFim
2012Aisha HumairaJarumaFim
2012'Yar MayeJarumaFim
2012Badi Ba RaiJarumaFim
2012AkirizzamanJarumaFim
2012Dare DayaJarumaFim
2012Wata Tafi WataJarumaFim
2013Da Kai Zan GanaJarumaFim
2013HaskeJarumaFim
2013Ban Sani BaJarumaFim
2014Mai Dalilin AureJarumaFim
2014Daga Ni Sai KeJarumaFim
2014Ali Yaga AliJarumaFim
2014BasajaJarumaFim
2014Uba Da 'DaJarumaFim
2014Indon KauyeJarumaComedy/Fim
2014Ba'asiJarumaFim
2014JarumtaJarumaFim
2017Gida da wajeJarumaFim
2017Ciki Da RainoJarumaComedy/Fim
2019Hawwa KuluJarumaFim
2019WakiliJarumaFim
2019Dan BirninJarumaFim
2019Gidan BadamasiJarumaComedy/Fim

Hotunagyara sashe

Duba nangyara sashe

Manazartagyara sashe

 1. "Hadiza Aliyu".
 2. All Africa. "Nigeria: I Had to Learn Hausa to Feature in Kannywood - Hadiza Gabon". Amina Alhassan and Mulikat Mukaila. Retrieved 28 December 2013.
 3. "I want to settle down – Gabon - Blueprint". Archived from the original on 2015-04-02. Retrieved 2015-03-10.
 4. "Gabon Official". Archived from the original on 2015-03-24.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
 5. "Hadiza Gabon - HausaFilms.tv".
 6. "Gabon Official". Archived from the original on 2015-03-24.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
 7. Elites, The (21 September 2017). "Famous Kannywood Actress Hadiza Aliyu Gabon, Debuts In Nollywood Movie". The Elites Nigeria. Retrieved 24 October 2019.
 8. "The trailer for Mike Ezuruonye's new movie 'Lagos Real Fake Life' isn't quite there yet » YNaija". YNaija. 10 October 2018. Retrieved 24 October 2019.
 9. Husseini, Shuaibu (12 November 2016). "Gold for Kannywood's shinning star, Hadiza Gabon, from Queensland". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News. Retrieved 24 October 2019.
 10. Lere, Muhammad (21 September 2017). "Kannywood: Hadiza Gabon features in first Nollywood movie - Premium Times Nigeria". Premiumtimenews. Retrieved 24 October 2019.
 11. "Hadiza Gabon - HausaFilms.tv".
 12. "HAG Foundation - Committed to Serving Humanity". HAG Foundation. Archived from the original on 2 February 2017. Retrieved 22 January 2017.
 13. "NASCON introduces Dangote classic seasoning into Kano market". Businessday NG. 17 December 2018.
 14. "NASCON launches New Dangote Classic Seasoning Cubes". NASCON launches New Dangote Classic Seasoning Cubes (in Turanci).
 15. "Brand Ambassador Market Tour". NASCON. 16 July 2019. Archived from the original on 10 August 2020. Retrieved 1 March 2021.
 16. "Hadiza Gabon enlivens IDP camp". Daily Trust. Ibrahim Musa Giginyu. Retrieved 19 March 2016.
 17. "Gabon Official". Archived from the original on 2015-03-24.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
 18. "Kannywood at the 2014 City People Entertainment Awards - Winners and Nominees [HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities]". hausafilms.tv. Retrieved 24 October 2019.
 19. "Linda Ikeji's Blog".
 20. "Premium Times Nigeria".
 21. "Hadiza Gabon, Usman Uzee honoured at African Hollywood Awards". Premium Times Nigeria. Mohammed Lere. Retrieved 6 November 2016.
 22. Agbon, Ehis (16 September 2017). "2017 CITY PEOPLE MOVIE AWARDS (NOMINEES FOR KANNYWOOD)". Procyon News. Archived from the original on 18 October 2019. Retrieved 24 October 2019.
 23. "Hadiza Aliyu Gabon on Instagram: Alhamdulillah ✌🏼️👌👌🏻". Instagram. Hadiza Aliyu Gabon. Retrieved 10 December 2016.
 24. "Was honored to be part of Startup Kano Women Conference.. Women empowerment gives me so much joy. Alhamdulillah". Twitter. Hadiza Aliyu. Retrieved 16 December 2016.
🔥 Top keywords: