Aisha Tsamiya

Ƴar'wasan fim ɗin Kannywood a Najeriya

Aisha Aliyu Tsamiya Wacce akafi sani da A'isha Tsamiya ta kasance jaruma a masana'antar funafinai ta Hausa kannywood.Ta yi fina- finai da dama irin su Ɗakin Amarya, Rayuwa Bayan mutuwa, Aisha Tsamiya bayan tayi dogon zango a masana'antar sai kwatsam aka ji za ta yi aure.

Aisha Tsamiya
Rayuwa
HaihuwaNasarawa (Nasarawa), 1992 (30/31 shekaru)
ƙasaNajeriya
Harshen uwaHausa
Karatu
MakarantaYusuf Maitama Sule University (en) Fassara
HarsunaTuranci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'aJarumi

Manazartagyara sashe

(An haife ta a shekara ta dubu daya da dari tara da cassa'in da biyu 1992A.C) Miladiyya . a ƙaramar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano a Arewacin Nijeriya. Tayi karatunta na firamare da sakandare a Giginyu. Sannan jarumar tayi karatunta a Jami'ar Yusuf Maitama Sule dake jihar Kano.[1] [2]A halin yanzu Aisha tsamiya tana cigaba da Neman ilimi domin kara habaka aikinta na shirya finafinai. Aisha Tsamiya tayi aure tare da mijin nata mai suna Alhaji Abubakar Buba a ranar 26/02/2022, sannan mijinta yakasance dan kasuwa kuma daya daga cikin jigajigan Yan siyasar jahar yobe kuma daya daga cikin na Hannun daman Gwamnan jihar Mai Mala Buni. A yanzu dai tana da shagon da ta bude na siyar da mayamayen gyaran fata kuma tana koyar da girke girme a shafinta na Tiktok.

Fina finan ta

1 Dakin amarya

2 Abba na

3 Tafin hannu

4 Jamila

5 Zinat

6 zarge

7 manyan mata da sauran su.

Tarihigyara sashe

Aisha Aliyu, wata matashiyar ƴar fim din Hausace da take da burin zama babba a harkar fim. An haifeta a ƙaramar hukumar Nasarawa dake jihar Kano. Tayi makarantar firamare da sakandare ta Giginyu kuma a halin yanzu tana kan cigaba da karatun ta ne tanada burin yin karatu mai zurfi.

Ta fara aiki ne a matsayin mai daukar nauyin fim ɗin ta da kanta saboda sha'awar fina-finai don isar da sako ga al'ummarta, saƙonni kan canjin zamantakewa. Fim dinta na farko shi ne Tsamiya daga nan sai wani fim mai suna Rabi’a, Rayuwa Bayan Mutuwa, Uzuri da Dakin Amarya.Hakika Aisha Tsamiya ta nuna wa duniya ita ba kanwar lasa ba ce, domin har yanzu tana ci gaba da bayyanar da hazaka da kwarewarta a fagen finafinan Hausa. Tsamiya ta zama daya daga cikin fitattun ƴan fim goma a cikin jaruman Kannywood a shekara ta 2016.[3] Hakanan Kuma Tsamiya na da masoya da mabiya masu ɗimbin yawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo.[4][5]

Aisha Aliyu tsamiya matashiyar 'yar fim ce data nuna bata da sha'awar shiga masana'antar da shirya fina finan hausa.

An haifi Aisha tsamiya a shekara ta dubu daya da darin tara da cassa'in da biyu 1992 a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano, ta tafi makarantar firamare ta Giginyu sannan ta halarci makarantar sakandire.

Fina-Finaigyara sashe

Ga jerin fina-finai da Aisha Aliyu (Tsamiya) ta ksance a ciki:

 • Tsamiya
 • Ranar Baiko
 • Hanyar Kano
 • Bahaushiya
 • Da Kishiyar Gida
 • Dakin Amarya
 • Husna
 • Jamila
 • Mai Dalilin Aure (Match Maker)
 • Makahon Gida
 • Munubiya
 • Niqab
 • Nisan Kiwo
 • Rayuwa Bayan Mutuwa
 • Zeenat
 • Kalan Dangi
 • Mijin biza
 • Abbana
 • Tafin hannu
 • salma
 • Manyan mata
 • Burin fatima
 • Dawo dawo
 • Mar'atussaliha

Aikigyara sashe

Aisha Tsamiya ta fara aiki ne saboda sha'awar da takeyiwa sana'ar shirya fina-finan Hausa a cewar ta domin isar da sako ga al'umma. Film din Tsamiya shine film din data fara suna a cikin shi, sannan ta fito a film din Rayuwa bayan Mutuwa, Uzuri, Dakin Amarya, kalan dangi da dai sauran su.

Aisha tsamiya ta zama matsayi na goma a shahararren film din salma, hakika har yanzun Aisha tsamiya tana daga cikin matan da tauraruwar su ta dade tana haskawa a masana'antar shirya fim na hausa, kuma ta kware sosai a wannan sana'ar ta shirya fina finan hausa.sannan tazamo daya daga cikin jaruman da ake mutumtawa saboda Bata shigar banza, ba,a taba ganinta da shigar da Bata dace ba ga addininta .Aisha tsamiya mace ce me natsuwa da Kamala da mutunci acikin jerin jaruman kanniwud watau masana,antar shirya fina finai na Hausa.

Ilimigyara sashe

A halin yanzu dai Aisha tsamiya tana cigaba da neman ilimi a arewa. Aisha tsamiya har yanzun jarumar tayi aure a shekarar dubu biyu da Ashirun da biyu (2022) Alu,mma da dama sun mata fatan alkhairi domin tanada masoya masu yawa kasancewarta jarumar da ake ganin mutuncinta a masana,antar kanniwud, A halin yanzun jarumar tana sana,a inda tabude shagon Abaya dogayan riguna na mata , sannan tana koyar da girke girken zamani a shafinta na TikTok.

Manazartagyara sashe

🔥 Top keywords: